ilimi
Satar Ɗalibai: Ganduje ya rufe Kwalejin Fasaha ta Bagauda
Gwamnatin jihar Kano ta bada umarnin rufe Kwalejin Fasaha ta Bagauda nan take.
Kwamishinan ilimin jihar Alhaji Sanusi Sa’idu Ƙiru ne ya sanar da hakan ta cikin wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ma’aikatar Aliyu Yusuf ya fitar a daren Litinin ɗin nan.
Sanarwar ta ce, an ɗauki matakin rufe Kwalejin ne saboda dalilan tsaro, a don haka ya zama dole Gwamnati ta kare rayukan ɗalibai da malamai da sauran ma’aikatan Kwalejin.
Kwamishinan ya nemi iyayen yara da su hanzarta kwashe ƴaƴan su daga makarantar tun daga yanzu.
A ƙarshe Kwamishinan ya yi godiya ga iyayen yara kan gudunmuwar da suke bai wa Gwamnati wajen aiwatar da tsare-tsaren ta da suka shafi tabbatar da tsaro.
Ko a watan Maris da ya gabata ma Gwamnatin Kano ta rufe wasu makarantun kwana, masu nisa da ƙwaryar birni saboda dalilan tsaro.
Wannan dai na zuwa ne yayin da ake samun rahotannin hare-haren ƴan bindiga a makarantu, tare da satar ɗalibai a wasu yankunan ƙasar nan.
You must be logged in to post a comment Login