Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Saudi Arabia – Iran ce ta kai mana hari

Published

on

Saudi Arabia ta fito fili ta gaya wa duniya cewa ba ta da wata tantama ko shakku a kan cewa kasar Iran ce ta kai mata hare-hare akan matatun manta.

 

Sai dai karamin ministan harkokin wajen kasar ta Saudiya Adel Al Jubeir, ya ce za su jira har sai an kammala cikakken binciken da ake yi yanzu kafin su tsayar da shawarar yadda za su mayar da martanin.

 

Ya ce martanin da za a mayar ya hada da na diflomasiyya, da tattalin arziki da kuma na soji.

 

Ministan ya kara da cewa, ‘kowa yana kokarin ya kauce wa yaki, kowa yana kokarin ya ga rigimar ba ta bazu ba. Saboda haka za su auna dukkanin zabin da suke da shi, daga nan za su yanke shawara a lokacin da ya dace.

 

Saudiyya dai na kokarin ganin ta kafa kwakkwara kuma tartibiyar hujja a kan babbar abokiyar gabar ta Iran a kan hare-haren.

 

Wasu da dama a kasar ta Saudiyyar na ganin mayar da martani na soji na daidai-wa-daida zai iya zama babban kashedi ga Iran din.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!