Manyan Labarai
Saudiyya:Ta ɗauki nauyin aiki ga jariran da aka haifa a manne
Gwamna Abba Kabir ya yi bankwana da wasu tagwayen da suke manne da juna domin yi musu aikin a ƙasar Saudiyya
Gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yabawa masarautar Saudiyya karkashin jagorancin Sarki Salman Bin Abdul’aziz kan daukar nauyin yi wa jarirai tagwaye a Kano tiyata a wani asibiti da ke kasar Saudiyya a birnin Riyadh
Wannan na ƙunshe ne ta cikin wata takarda da ɗauke da sa hannun sakataren yaɗa labaran Gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa ya kuma rabawa manema labarai
Da yake jawabi a lokacin da yake bankwana da iyayen tagwayen jarirai a filin jirgin sama na Aminu Kano, gwamnan ya bayyana irin alherin da Sarki Salman ya yi a matsayin wani aiki da Allah ya saka masa da ya dace a yi koyi da shi
Gwamna Yusuf wanda ya yi addu’ar Allah ya dore da dankon zumuncin da ke tsakanin Kano da Masarautar Saudiyya, ya bayyana cewa gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba a kokarinta na dawo da martabar da aka rasa a bangaren kiwon lafiya a jihar
Gwamnan ya kuma ce ba da daɗewa ba Likitocin Saudiyya sunzo Asibitin Koyarwa na Aminu Kano, domin kula da marasa lafiya da ke fama da ciwon zuciya da matsalar idanu kyauta
Don haka ya yi addu’a ga jariran tagwayen da suke hade da juna don samun nasarar aikin tiyatar da aka yi musu sannan kuma suka dawo da rai a matsayin mutane biyu masu zaman kansu
Da yake jawabi tun da farko, karamin jakadan Saudiyya a Kano, Sheikh Khalil Al’adamawi ya bayyana cewa, irin wannan shiri na nuni ne da yadda Saudiyyar ta himmatu wajen gudanar da ayyukan jin kai da kuma sadaukar da kai wajen taimakon mabuƙata
Ya kuma kara da cewa, ana mika wannan karamcin ne ga mabukata ba tare da la’akari da kasarsu ko asalinsu ba, yana mai jaddada cewa masarautar Saudiyya ce kan gaba wajen samar da kayayyakin jin kai na kasa da kasa
Daga nan ne karamin jakadan ya bayyana cewa za a kwantar da iyayen tagwayen da suka hade a birnin Riyadh, kuma za a ba su tsarin tallafi don samun kwanciyar hankali da taimako a tsawon tafiyar su
A nasa jawabin, mahaifin tagwayen da suka a haɗe, Malam Hassan Isa Kano ya bayyana matukar godiyar sa ga mai kula da masallatai biyu masu tsarki, Salman Bin Abdulaziz bisa daukar nauyin yi wa tagwayen, Hassana da Husaina aikin tiyata, yana mai addu’ar Allah ya jikansa ya saka masa da iyalansa da jannatul Firdausi
Ya kuma yabawa gwamnan jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf bisa kauna da kulawar da ya nuna musu tare da ba su lokaci domin yi musu bankwana a filin jirgin sama a yau
You must be logged in to post a comment Login