Labarai
SERAP ta yi barazanar gurfanar da ‘yan majalisu da gwamnoni a gaban kotu
Kungiyar da ke rajin tabbatar da daidaito da gaskiya a ayyukan gwamnati SERAP ta yi barazanar gurfanar da majalisun dokokin tarayyar kasar nan da kuma kungiyar gwamnonin arewa matukar aka aiwatar da dokar sanya idanu kan kafafen sada zumunta.
Kungiyar ta SERAP ta bayyana hakan ne ta cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na twitter.
A cewar kungiyar ya zama wajibi ta dauki wannan mataki don dakile yunkurin da gwamnonin arewa da kuma majalisun dokokin tarayya ke yi don kafa dokar da za ta takaita ‘yancin da ‘yan kasar nan ke da shi a shafukan sada zumunta.
Tun farko dai gwamnonin na arewa yayin wani taro da suka gudanar jiya a Kaduna, sun ce, daukar wannan mataki ya zama wajibi saboda yadda aka yi amfani da shafukan sada zumunta don yada karairayi yayin zanga-zangar kin jinin ‘yan sandan SARS.
You must be logged in to post a comment Login