Labarai
Shalkwatar soji na shirin sauya wa wasu manyan jami’ai wuraren aiki

Shalkwatar rundunar sojin kasar nan ta ce za ta sauya wa wasu daga cikin manyan jami’anta wuraren aiki, a wani bangare na kara inganta ayyukanta da harkokin tsaron kasar nan.
Babban hafsan sojin Lutanan Janaral Olufemi Oluyede ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da mai rukon mukamin shugaban sashin yada labarai na rundunar Lutanan Kanal Appolonia Anele ta fitar.
Haka kuma shalkwatar ta ce, za ta ci gaba da sauyawa duk sauran jami’anta wuraren aiki.
You must be logged in to post a comment Login