Manyan Labarai
Shan dumi lokacin sanyi na kawo gobara – Saidu Muhammad
Kakakin hukumar kashe gobara na jihar kano Alhaji Sa’idu Muhammad ya ja hankalin Al’ummar jihar nan da su maida hankali wajen kashe wuta a lokacin da suke jin dumi a lokacin sanyi.
Haka kuma yace iyaye su sa Ido sosai akan ‘ya’yansu domin suna shiga da wuta danki a lokacin sanyi.
Kakakin ya bayyana haka ne lokaci da wakilinmu Shamsu Da’u Abdullahi yake zantawa dashi a kan hanyoyin da za’abi wajen magance matsalar gobara a lokacin sanyi.
Ya kara da cewa yana kira da ‘yan kasuwa dasu rika gayawa masu gadin kasuwa dasu rika kashe wuta a lokaci da suke jindumi a lokacin sanyi.
Wasu mutane da wakilin mu ya zanta dasu akan yanda zasu rika kashe wuta yayin lokacin jin dumi
Wasu sun ce sukan kashe wutar ne da ruwa bayan shan dumi yayin da kuma was uke cewa suna barin ta ne ta zama toka.
Wakilin mu Shamsu Dau Abdullahi ya rawaito cewa hukumar tana kira da ‘yan kasuwa da su rika sa ido sosai akan masu saida kayan abinci da masu saida shayi wajen kashe wuta yayin da zasu tashi a kasuwa.