Kasuwanci
Sharhi: Dakatar da zirga-zirgar jiragen kasa zai gurgunta tattalin arzikin Najeriya – Dakta Shamsuddeen
Masanin tattalin arziki a sashen tsumi da tanadi na jami’ar Bayero a Kano ya ce, dakatar da zirga-zirga jiragen kasa a Najeriya zai jawo nakasu a tattalin arziki.
Dakta Shamsuddeen Muhammad ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radiyo.
Masanin ya ce ’’idan muka yi duba da yadda shugaban kasa Muhammudu Buhari yayi kasafin kudin bana ya ta’allaka ne akan kudaden da sufarin jiragen kasa za su samar”.
“Bawai iya kadai jiragen zai shafa ba hatta da masu siye da siyarwa a tashoshin jiragen za su samu koma baya a harkokin kasuwancin su”.
Ya ci gaba da cewa “hatta da ƴan dako a tashoshin zasu fuskanci matsin rayuwa sakamakon rashin aikin yi dalilin dakatar da zirga-zirga jiragen”.
Wannan na zuwa ne bayan da aka kai wasu tagwayen hare-hare akan jiragen kasa dake tafiya akan hanyar Abuja zuwa Kaduna a baya-bayan nan
You must be logged in to post a comment Login