Sharhi
Sharhi: Idan ‘yan siyasar ƙasar nan ba su bi a hankali ba, za su sanya ƙasar cikin hatsarin siyasa – Farfesa Kamilu Fagge.
Masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke nan Kano, ya bayyana cewa idan har ‘yan siyasar Najeriya ba su yi taka tsan-tsan ba to kuwa za su iya sanya kasar cikin hatsarin siyasa.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ne ya bayyana hakan a zantawar sa da Freedom Radio.
Fagge ya ce, wannan Mataki da ko wanne bangare na kasar ya dauka ya nuna shirin fara tunkarar zaben shekarar 2023 mai zuwa.
“Yadda alkiblar kasar ta nuna a yanzu ya nuna cewa, duka bangarorin Najeriya sun shirya tunkarar zabukan 2023,”
“Idan ya kasance kowanne bangare ya ja zare lallai sai dan takarar shubagan kasa ya fito daga yankinsa hakan yayi nuni da yadda siyasar Najeriya ke samun armashi,”
“Hatsarin kuma shine muddin wasu suka fara nuna wariya da nuna kabilanci da kuma rikicin addini shakka babu wannan ya nuna kasar ba ta koyi darasi daga abin da suka faru a baya na fadace-fadace da hakan yayi sanadiyyar tarwatsewar mulkin dimokuradiyya” a cewar Farfesa Kamilu Fagge.
Wannna dai na zuwa ne bayan da aka jiwo kungiyar dattawan arewacin Najeriya na bayyana cewa babu wanda zai tilasta wa al`ummar yankinta zabar wani dan takarar shugaban kasa da ya fito daga kudancin kasar a zaben shekarar 2023.
Kamar yadda kakakin kungiyar Dakta Hakeem Baba Ahmed ya shaida wa BBC cewa yankin arewa nada yawan masu zabe, don haka ‘yankin ba ya shakkar ko wace irin barazana.
Haka zalika shima tsohon gwamnan jihar Imo, Sanata Rochas Okorocha an jiyo shi na goyon bayan gwamnonin kudancin Najeriya kan batun mayar da kujerar shugaban kasa yankin.
You must be logged in to post a comment Login