Labarai
Sharhi: Raina umarnin kotu ne yin tankiya ga hukuncinta – Farfesa Kamilu Fagge
Masanin siyasa a Kano Farfesa Kamilu Sani Fagge ya ce, raina umarnin kotu ne yadda wasu yan siyasa ke musanta hukuncin ta.
Farfesa Kamilu Sani Fagge ya bayyana hakan a zantawarsa da wakiliyarmu Safara’u Tijjani Adam.
Farfesan ya ce, “Mulkin dimukradiyya an gina shi a kan doka da oda, duk kankantar kotu in ta bada umarni ko hukunci dole a yi biyayya, duk girman mutum duk mukamin sa”.
“Rashin sanin doka ne ya sanya ake yin yar tankiya tsakanin kotu da wasu masu riki da madafun iko, domin kuwa idan kotu ta yi hukuncinta babu abinda ya ragewa mutum sai yin biyayya sai dai idan bai gamsu ba sai ya daukaka kara”.
Wannan dai na zuwa ne baywan da wata babbar kotu a Abuja ta yi watsi da bukatar da bangaren jam’iyyar APC a nan Kano tsagin gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya shigar gaban ta na neman ta yi watsi da hukuncin data zartar a baya kan zaben shugabancin jam’iyyar a ranar Alhamis.
You must be logged in to post a comment Login