Labarai
Shari’ar neman hakki na neman gagarar talaka – Barista Badiyya
Kungiyar lauyoyi ta kasa reshen jihar Kano ta bayyana fargabar ta kan Karin kudaden cike takardun rantsuwa da na shigar da kara da sauran abubuwan da suka shafi ‘yan sanda.
Barista Badiyya Abdullahi Mua’zu ce ta yi wannan korafi ta cikin shirin ‘yanci da rayuwa na nan Freedom Radio.
Barista Badiyya ta ce abin fargabar ma shine yadda wannan matsala zata iya shafar talaka kai tsaye, ta yadda ba zai iya shigar da kara ba ko da kuwa an zalunce shi.
Barista tace a da ana sayar da takardar ranstuwa ta Affidavit akan naira dari biyu amma a yanzu ya kai naira dubu shida.
Labarai masu alaka:
Rana zafi : Ƴan shara sun shiga yajin aiki a Kaduna
Rashin adalci a shari’a shi ke haifar da matsaloli – KCSF
Ta kuma ce abin takaicin kuma shine babu wata doka da ta bada damar kara wannan adadin kudi da yawa haka.
To sai dai da ya ke mayar da jawabi ta cikin shirin, kakakin babbar kotun jihar Kano Baba Jibo Ibrahim ya ce Karin kudin na nan kunshe cikin kundin doka.
Ya ce su kansu Karin ya tayar musu da hankali, kasancewar idan aka tafi a haka, to kuwa shari’a zata iya gagarar talaka, amma dai abu ne da za’a a iya gyarawa.
You must be logged in to post a comment Login