Kiwon Lafiya
Shelkwatar rundunar ‘yan sanda ta kasa ta musantar zargi canza CP wakili
Shalkwatar rundunar ‘yan sanda ta kasa musanta rade-raden da ake yadawa kan sauyawa kwamishinan ‘yan sandar jihar Kano Mohammad Wakili wurin aiki ba gaskiya ba ne.
Majiyar ta bayyanawa jaridar Daily Nigerian cewar duk da bukatar cire kwamishinan yan sanda da gwamnan jihar Kano yayi, shelkwatar ‘yan sanda jihar Kano ta ce babu wani dalilin da zai tabbatar da cire kwamishinan daga kujerarsa ba.
Jaridar Solacebase ta ce a jiya ne dai mai martaba sarkin Kano Muhammad Sunusi da yake zantawa da manema labarai dangane da zabukan da aka gudanar a ranar asabar da gwamnoni da yan majalisun jihohi, ya yabawa hukumomin tsaro da suka tabbatar da zaman lafiya kafin da bayan zaben.
Inda mai martaba yake mika godiyarsa ga kwamishinan yan sanda ta jihar Kano na irin jajircewarsa tare da hadin kan da al’ummar jihar Kano suka bayar wajen tabbatar da hakan, yake cewa tabbas kwamishinan ‘yan sandan ya cancanci yabo.
Wannan yabo dai na zuwa bayan jajircewar CP Wakili wajen kawar da hargitsi da tashe-tashen hankula a yayin zabe, baya ga nuna kwarewarsa na yin gaskiya tare da kauracewa sonka a yayin zabuka shugaban kasa da na gwamnoni.
Wata majiyar mai karfe ta bayyanawa jaridar Daily Nigeria cewar kwamishina yan sanda yayi aiki da hukumar yan sanda na shekaru 32, kuma yake daf da yin ritayarsa sakamakon shekarunsa a 15 ga watan Mayu wannan shekara, kuma kwamishinan na nan a jihar Kano har zuwa lokacin ritayarsa.