Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Shelkwatar rundunar ‘yan sanda ta kasa ta musantar zargi canza CP wakili

Published

on

Shalkwatar rundunar ‘yan sanda ta kasa musanta  rade-raden da ake yadawa kan  sauyawa kwamishinan ‘yan sandar jihar Kano Mohammad Wakili  wurin aiki ba gaskiya ba ne.

Majiyar ta bayyanawa jaridar Daily Nigerian cewar duk da bukatar  cire kwamishinan yan sanda da gwamnan jihar Kano  yayi, shelkwatar ‘yan sanda jihar Kano ta ce babu wani dalilin da zai tabbatar da cire kwamishinan daga kujerarsa ba.

Jaridar Solacebase ta ce a jiya ne dai mai martaba sarkin Kano Muhammad Sunusi da yake zantawa da manema labarai dangane da zabukan da aka gudanar a ranar asabar da gwamnoni da yan majalisun jihohi, ya yabawa hukumomin tsaro da suka tabbatar da zaman lafiya  kafin da bayan  zaben.

Inda mai martaba yake mika godiyarsa ga kwamishinan yan sanda ta jihar Kano na irin  jajircewarsa tare da hadin kan da al’ummar jihar Kano suka bayar wajen tabbatar da hakan, yake cewa tabbas kwamishinan ‘yan sandan ya cancanci yabo.

Wannan yabo dai na zuwa bayan jajircewar CP Wakili wajen kawar da hargitsi da tashe-tashen hankula a yayin zabe, baya ga nuna kwarewarsa  na yin gaskiya tare da kauracewa sonka a yayin zabuka shugaban kasa da na gwamnoni.

Wata majiyar mai karfe ta bayyanawa jaridar Daily Nigeria cewar kwamishina yan sanda yayi aiki da hukumar yan sanda na shekaru 32, kuma yake daf da yin ritayarsa sakamakon shekarunsa a 15 ga watan Mayu wannan shekara, kuma kwamishinan na nan a jihar Kano har zuwa lokacin ritayarsa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!