Kiwon Lafiya
Shiga yajin aiki saɓa alƙawarin da muka yi ne – Martanin Gwamnati ga likitoci
Gwamnatin tarayya ta yi watsi da shirin tsunduma yajin aikin na ƙungiyar likitoci a yau Litinin.
A wata sanarwa da ma’aikatar Ƙwadago ta ƙasa ta fitar, a yammacin Lahadi, ta ce Gwamnatin tarayya tana bin yarjejeniyar da suka ƙulla da ƙungiyar a ranar 21 ga watan Agustan da muke ciki.
Sanarwar mai ɗauke da sa hannun jami’in yaɗa labaran ma’aikatar Charles Akpan ta ce, matakin da likitocin suka ɗauka ya saɓa da abin da aka cimma a yarjejeniyarsu da Gwamnati a baya.
Mista Akpan ya ce, Gwamnatin tarayya na aiwatar da ɓangarenta na yarjejeniyar tare da sanya idanun ministan ƙwadago. A yau Litinin ne ƙungiyar likitocin ta ƙasa ta ayyana shiga yajin aikin gargaɗi na makonni uku. Shugaban ƙungiyar na ƙasa Farfesa Innocent Ujah ne ya sanar da hakan, bayan babban taronta na ƙasa a birnin Benin na jihar Edo.
Ƙungiyar likitocin ta ce, tsunduma yajin aikin ya zama dole, sakamakon gaza cimman buƙatunta da Gwamnatin tarayya ta yi.
You must be logged in to post a comment Login