Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

Ba tabbas akan injin motocin tsere na Ferrari

Published

on

Mahukuntan gudanar da gasar tseren motoci na Formula 1, sun ce    basu da tabbas akan cewar injin motocin  kamfanin Ferrari  sun cika sharuda , kasancewar bin diddigin hakan abu ne mai wahala matuka.

Hakan ya biyo bayan zargin da wasu kungiyoyin gasar  guda bakwai suka shigar gaban hukumar tsara gasar FIA, inda suka nuna rashin jin dadin su da halin ko  in kula da akayi da lamarin.

Labarai masu alaka.

Dalilan dakatar da wasanni a birnin Tokyo

Aruna Quadri ya tafi jinyar rauni na mako uku

 

Sai dai hukumar ta FIA, ta bayyana matsayar ta in da tace duk wani mataki da za’a dauka da kuma bincike ba zai iya karkarewa a kusa ba, kasancewar ba cikakku kuma gamsassun hujjoji  na karya ka’idojin yin gasar da kamfanin na Ferrari ya yi.

A larabar data gabata, kungiyoyin bakwai a sanarwar da suka fitar sun nuna rashin jin dadin su dangane kamfanin Ferrari, in da suka kara dacewa rashin bincika lamarin zai saka musu shakku kan , jagoranci nagari, adalci da tsari na hukumar ta keyi.

Haka kuma, sun kara da cewa suna da ikon a yi musu bayani dalla-dalla dangen da zargin su wada hakan kadai zai cire shakkun dake tattare dasu.

 

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!