Labaran Kano
Shin me zaku iya tunawa game da rayuwar marigayi jarman Kano
A yau ne shahararran dan kasuwar nan da ya samar da kamfanin Jirgin sama mai zaman kansa na farko a kasar nan marigayi Alhaji Muhammad Adamu Dan Kabo ke cika shekaru goma sha takwas da rasuwa.
Marigayi Dan Kabo dai ya kasance mutum jajirtacce mai son ci gaban al’umma da kuma tallafawa tattalin arziki, wanda rashin say a zama babbar asara ga al’umma baki daya.
An dai haifi marigayi Alhaji Muhammad Adamu Dan Kabo a ranar uku ga watan Afrilun shekarar 1942, a karamar hukumar Kabo dake nan jihar Kano, inda yayi karatun Alkur’ani a garin na Kabo.
Alhaji Dan Kabo ya kasance dan kasuwa da ya samar da masana’antu daban- daban a kasar nan tare da samar da jirgin Sama na Kabo Air a shekarar 1980 wanda ya fara aiki a shekarar 1981.
Kafin rasuwar tasa kamfanin jirgin sama na Kabo ya mallaki jirage guda Ashirin da suke aiki da jigilar mutane a kwacce rana a sassan kasar nan musamman ‘yan kasuwa dake gudanar da kasuwanci a nan jihar Kano tare da tafiye tafiye dan shigo da kaya wanda hakan yasa kasuwancin jihar Kano ya habbaka tare da yin dai-dai da kasuwancin zamani.
Da ya ke jawabi Laftanan Kanal mai ritaya Daudu Sulaiman da ya kasan ce aboki ga marigayi Dan Kabo lokacin da yana raye ya ce, marigayi Muhammadu Adamu Dan Kabo mutum ne mai matukar son jama’a da son ci gaban su, wanda kuma ya kasance mutum mai alkahiri ga jama’a,wanda dukiyar sa bata rufe masa idanu ba.
Da yake jawabi game da yadda marigayi Dan Kabo ya gudanar da rayuwar sa tsohon shugaban tsangayar koyar da aikin jarida na jami’ar Bayero Farfesa Balarabe Maikaba da ya rubuta littafi kan rayuwar marigayin cewa yayi kamata yayi gwamnati ta farfado da kamfanin na Dan Kabo duba da yadda ya durkushe a halin yanzu, don samar da kudin shiga ga jihar Kano, tare da sanya sunan sa a wasu gurare da za’a dinga tunawa da shi, la’akari da ayyukan alkhairi da ya gudanar a lokacin yana raye.
Hasiya Muhammad Adamu Dan Kabo itace kasance babbar ‘ya ga marigayin ta ce mahaifin ta mutum ne da baya nuna banbanci a tsakanin yayan sa da ‘ya’yan wasu daban, kuma ya sadaukar da rayuwar sa wajen tallafawa duk mutumin daya fuskanci yana cikin matsi na rayuwa a ko’ina yake.
Al’ummar jihar Kano da dai na ci gaba da bayyana cewa lokacin da Dan Kabo na raye ya bada gudun mawa sosai ga musulman kasar nan wajen saukaka musu kudin jirgi lokaci tafiya aikin hajji da umrah wanda hakan babban abin a yaba ne da kuma samun tarin lada.
A ranar hudu ga watan Afrilun shekarar 2002 ne dai aka wayi gari da samun labarin rasuwar Dan Kabo, kwana daya Tsakani da lokacin bayan da aka gudanar da bikin cikar sa shekaru 60 da haihuwa, wanda mutuwar tasa tazowa al’ummar kasar na a bazata, ta kuma tilasta musu shiga cikin halin dimuwa.
You must be logged in to post a comment Login