Sharhi
Shin Shugaba Buhari zai yi koyi da Obasanjo wajen sabawa tsarin mulki da yin tazarce a shekarar 2023?
Tun bayan kammala babban zaben Najeriya a shekarar 2019 hankali ya karkata ga wani zaben da ake sa ran gudanar wa a shekarar 2023.
Kamar yadda tsarin mulkin Najeriya ya tanada tsawon wa’adin shugaban kasa ko Gwamna shine ya shekara takwas bayan yayi nasarar zabe a karo na biyu.
An dai zabi shugaba Muhammadu Buhari a karo na farko a ranar 28 ga watan Maris na shekarar 2015 yayin da ya kammala wa’adin sa na farko a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar da muke ciki .
Shugaba Muhammadu Buhari ya sake karbar rantsuwa a wa’adi na biyu a ranar 29 ga watan Mayu na shekarar bana.
Ana sa ran shugaba Muhammadu Buhari zai kammala wa’adin da tsarin mulki ya tanadar masa a ranar 29 ga watan Mayun shekarar 2023.
Amma a ‘’yan kwanakin nan ma sai da fadar shugaban kasa ta musanta cewa shugaba Buhari baya neman karo na uku a mulkin Najeriya wanda hakan ya sabawa tanadin kundin tsarin mulkin.
Ko da yake sashen da yayi magana akan wa’adin da Gwamna ko shugaban kasa yayi yace “Gwamna ko shugaban kasa ba zai sake tsayawa takara ba muddin an zabe shi sau biyu a baya”.
Musanta neman wa’adi na uku da fadar shugaban kasa tayi ,a iya cewa yazo a wata gaba da shugabannin Najeriya suka rika yi ,da an fito an bayyana cewa ana kiraye kirayen su nemi karo na uku ko fiye da waadin da tsarin mulki ya tanada .
Tarihin neman tazarce ba bisa kaida ba a Najeriya ba sabon abu ba ne tsakanin shugabannin Najeriya da na Afrika.
Shugabannin Najeriya da dama ba na farar hula kawai ba, an zarge su da darewa akan mulki da kuma neman dawwama amma hakar su ba ta cimma ruwa ba.
Janar Yakubu Gowon ya shekara tara cif yana mulkin Najeriya ,har aka alakanta hakan da neman ya dawwwama a mulkin Najeriyar,dadewar janar Yakubu Gowon ta saka sojoji karkasahin jagorancin Manjo Janar Shehu Musa Yar’adua suka tumbuke Gwamnatin Janar Yakubu Gowon ,sannan suka nada Janar Murtala Muhammad a ranar 29 ga watan Yuli na shekarar 1975.
Bayanai sun nuna cewa san dafewa a karagar mulki dabi’a ce ta shugabannin Afrika , amma tarihi ya nuna cewa shugabannin Najeriya masu kokarin wuce waadin su basu cika nasara ba.
Idan ka duba bayan shugaba Marigayi Alhaji Shehu Shagari da ya yi nasarar lashe zaben shekarar 1983,Manjo janar Muhammadu Buhari da ya gaje shi bai jima ba domin watan sa 20 kacal a karagar mulki jamian fadar sa suka tumbuke shi daga kan mulkin Najeriya .
Wanda ya jagoranci juyin mulkin ya kuma hambarar da Manjo janar Muhammad Buhari a ranar 26 ga watan Agustan shekarar 1985 ,wato babban Hafsan sojan kasa Manjo janar Ibrahim Badamasi Babangida ya zama shugaban kasa inda ya kai tsawon shekara takwas .
Shekaru takwas da shugaba Babangida yayi yana kan karagar mulki ta hana shi cika alkawarin mika mulki ga farar hula da soke zaben shugaban kasa wanda ake zaton Marigayi Chief Moshood Abiola ya lashe, hakan ta tilastawa shugaba Babangida barin mulkin Najeriya.
Shirin tazarce na shugabannin na Najeriya ya kara ta’azzara zamanin mulkin marigayi Janar Sani Abacha , Janar Sani Abacha a zaben kasar nan da aka shirya a watan Agustan shekarar 1998 , jamiyyun siyasar Najeriya guda biyar da suka hada da UNCP da DPN da NCPN da CNC da GDM sun tsayar da janar Sani Abacha a matsayin dantakarar san a shugaban kasa.
Amma kafin gudanar da zaben Allah yayiwa janar Sani Abacha rasuwa , babban hafsan tsaro Janar Abdulsalami Abubakar ne ya gaji Janar Sani Abacha ,amma bai yi yunkurin zarcewa a kan mulkin Najeriya ba, ya mika mulki ga farar hula kuma ga tsohon soja kuma tsohon shugaban kasa Janar Olusegun obasanjo.
Cif Olusegun Obasanjo yayi waadi biyu inda aka zabe shi a ranar 27 ga watan Fabrairun shekarar 1999 aka kuma sake zabar sa a ranar 19 ga watan Afrilun shekarar 2003.
Rade radi sun fara bayyana a farkon shekarar 2004 jim kadan bayan fara waadin shugaba Obasanjo na biyu inda ya fada a wata kasar waje cewa yan samun matsin lamba daga wasu mutane cewa ya nemi karo na uku a mulki.
Daga nan ne alamu suka fara bayyana cewa tsohon shugaba Olusegun Obasanjo da gaske yake , an kai kudurin neman yiwa tsarin mulkin Najeriya kwaskwarima a shekarar 2006 wanda majalisar tarayya tayi watsi da shi aranar 16 ga watan Mayu na shekarar 2006.
An tilastawa shugaba Obasanjo ya bar mulki bayan da majalisa tayi fatali da neman ta canja tsarin mulki da zai bashi damar yin wa’adi na uku.
Mika mulki ga Marigayi Umar Musa Yar’adua a ranar 29 ga watan Mayu ya bude wani sabon shafi a tarihin Najeria inda a karo na farko farar hula suka mika mulki ga farar hula.
Marigayi shugaba Umaru Musa Yaraduwa ya rasu ranar 5 ga watan Mayun shekarar 2010, rasuwar Yaradua ta sa kafin ayi zaben sa a karo na biyu wanda ya gaje shi kuma tsohon shugaban kasa Goodluck Jonathan ya nemi zabe karo na farko a shekarar 2011 kuma ya lashe ,amma da ya tashi neman karo na biyu ya fadi wanda shi ne karo na farko da a Najeriya dan adawa ya kawar da shugaba mai ci.
Wannan maganganu da ke faruwa na musanta zargi da fadar shugaban kasa tayi na cewa shugaba Buhari na neman waadi na uku, lokaci ne kawai zai nuna.
Shugabannin Najeriya maganganu su kan faru akan suna aiwatar da wasu manufofi tun ana rade radi sai hakan ya zama gaskiya.
Ko shugaba Buhari zai zarce ko ba zai zarce ba, lokaci ne zai nuna domin a wa’adin sa na biyu da ya fara a kwanakin nan ko shekara daya ma bai kai ba.