Labarai
Shirin ACReSAL ya ƙaddamar da taron masu ruwa da tsaki na jihohi 7

Shirin kare muhalli da inganta aikin gona da sarrafa albarkatun Ruwa da rage illolin sauyin yanayi da daƙile zaizayar ƙasa, a yankunan da ke fama da ƙamfar Ruwa watau ACReSAL, ya fara gudanar da taron bita na kwanaki uku da masu ruwa da tsaki domin tattauna yadda za a ƙara inganta ayyukansa da kuma irin abubuwan da yankunan da ake gudanar da shi.
Shirin na ACReSAL wanda ya kasance na haɗin gwiwa tsakanin Bankin Duniya da gwamnatin tarayya da kuma gwamnatocin jihohi, ya fara gudanar da taron ne yau Litinin a nan Kano, ta hanyar tattara masu ruwa da tsaki daga jihohin bakwai na Arewacin ƙasar nan domin yin taza da tsifa kan ayyukan da shirin ke gudanarwa domin ƙara sanya sabbin abubuwan da al’umma ke buƙata.
Da ya ke jawabi ga manema labarai yayin taron, shugaban shirin na ACReSAL na ƙasa Abdulhamid Umar, wanda ya samu wakilcin shugaban sashen kula da harkokin albarkatun Ruwa na shirin Malam Shatima Adam, ya ce, sun zauna ne domin karɓar bayanai daga wajlkilan al’umma don sanin irin ayyukan da shirin zai gudanar domin bunƙasa ci gaban jama’a.
A nasa jawabin, shugaban, shugabannin shirin na ACReSAL na ƙasar nan Dakta Ibrahim Kabir, ya bayyana cewa shirin na ACReSAL na gudana ne ƙarƙashin wasu muhimman tsare-tsare, wanda ta hanyar bin su ne mutane ke cin gajiyarsa.
Taron dai, ya samu halartar masu ruwa da tsaki da dama ciki har da Hakimin Sumaila Alhaji Aminu Abdullahi Nasidi da masana da dama a fannin muhalli da aikin gona da sauransu.
You must be logged in to post a comment Login