Connect with us

Labarai

Majalisar Dokokin Kano ta bukaci masu iƙirarin mallakar filayen gwamnati su gabatar da takardun su

Published

on

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta bukaci mutanen da ke ikirarin mallakar filayen hukumomin gwamnati da su gabatar da takardun da ke tabbatar da mallakarsu.

Shugaban kwamitin da Majalisar ta kafa domin binciken filayen hukumar KNARDA da KASCO, kuma Mataimakin shugaban Majalisar Muhammad Bello Butu Butu, ne ya bayyana hakan.

Ya ce wasu daga cikin filayen an raba su ne a baya ba tare da cikakkun takardun mallaka ba.

Don haka ya bukaci duk wanda ke ikirarin mallakar wani fili, ciki har da wadanda suka gada daga iyayensu, da su gabatar da hujjojin da za su tabbatar da sahihancin mallakar.

Kwamitin zai tabbatar da cewa ba a ci gaba da mamaye ko kutsawa cikin filayen da ke karkashin mallakar hukumomin gwamnati ba.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!