Labarai
Gwamna Nasir Idris ya kai ziyara Tsamiya bayan hare-haren ƴan bindiga

Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris Kauran Gwandu, ya ziyarci al’ummar Tsamiya da ke Karamar Hukumar Bagudo domin jajanta musu kan hare-haren ’yan bindiga da aka kai wasu sassan yankin.
Wata sanarwar da Mai Bai wa Gwamnan na Jihar Kebbi Shawara kan Harkokin yaɗa labarai Yahaya Sarki, ya fitar ce ta bayyana wannan kai ziyara.
Sanarwar ta ce gwamnan ya yi Allah wadai da hare-haren, tare da bayyana cewa gwamnatin jihar ta ɗauki matakan magance matsalar tsaro kuma za ta ci gaba da aiki da hukumomin tsaro domin kare al’umma.
Gwamnan ya ce ya zaɓi zuwa yankin da kansa domin jajanta wa al’ummar maimakon tura tawaga.
A yayin ziyarar, Hakimi Muhammadu Wankai ya nemi gwamnatin jihar ta duba yiwuwar gyara hanyar Kaoje zuwa Illo zuwa Lolo.
You must be logged in to post a comment Login