Barka Da Hantsi
Shirin Barka da Hantsi 14-06-2022
Shirin yayi duba ne kan muhimmancin wannan rana ta 14 ga wata Yuni, da ta kasance ranar bayar da gudunmowar jini ta duniya, da hukumar lafiya ta majalisar ɗinkin duniya WHO ta ware domin haska muhimmancin bayar da gudunmowar jini domin taimakekeniyar ceton rai da sauran batutuwa masu alaƙa.
Baƙin da aka tattauna dasu, sun haɗa da Dr. Ɗalha Halliru Gwarzo, Ƙwararren likitan jini da ƙarin jini a kimiyyance daga Jami’ar Bayero da kuma Asibitin koyarwa na Aminu Kano. Sai kuma Abdullahi Sani, maga-takardan kwamitin ilimi na ƙungiyar ɗaliban dake karantar likitanci a asibin na Aminu Kano.
You must be logged in to post a comment Login