Bidiyo
Shirin Kowane Gauta 13-07-2022
A cikin shiri na Kowane Gauta muna tafe da kunshin wadannan labaran harma da karin wasu labaran
Duk da ikirarin babban Managan Darakta na kamfanin mai na kasa NNPC, cewa karanci da tsadar man fetur zai zamo tarihi, dillalen man fetur sun daga farashin lita fiye da yadda gwamnati ta kayyade. Tsohon Sakataran Gwamnatin tarayya Babachir Lawal yace daukar dan takarar mataimakin Tinubu a jam’iyyar APC da yazo da tsarin Muslim Muslim tiket, babban kuskure ne da ka iya jefa jam’iyyar halin kaka nakayi a lokacin zabe. Dan takarar Shugabanci kasa na jam’iyyar NNPP, Sanatan Rabi’u Musa Kwankwaso yace Jam’iyyun PDP da APC sun gama lalacewa zuwa ga matakin da bazasu iya kafa Gwamnati ba.
You must be logged in to post a comment Login