Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

KannyWood

Muhimman abubuwan dake faruwa yanzu haka a Kannywood

Published

on

 Abinda ya sa Adam Zango ya fasa zuwa Kano

Fitaccen jarumin fina-finan Hausar nan Adam A. Zango ya ce ya janye kudurin sa na zuwa jihar Kano domin kallon shirin Mati a Zazzau tare da masoyan sa.

Adamu Zango ya janye zuwan nasa ne, biyo bayan labarin da aka rika yadawa na cewa hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta shirya tsaf domin cafke shi da zarar ya shigo Kano.

Tun da farko dai Jaruma Rahma Sadau ce ta wallafa wani bidiyo da Jarumin yake bayanin cewa yana nan tafe a ranar lahadin wannan makon domin zuwa kallon shirin Mati a Zazzau a Kano.

Mujallar Kannywood Exclusive ta tuntubi shugaban hukumar tace fina-finai ta jihar Kano, Isma’il Na’abba Afakallah don jin gaskiyar labarin cewa ko hukumar na da shirin cafke Adamun da zarar ya shigo Kano.

Afakallah ya ce, duk mutumin da ya yadda zai mutunta mutanen Kano dole ne ya yarda ya bi dokokin su wanda majalisa ta tabbatar da su tun shekara ta 2001.

“Duk mutumin da bai yarda da wannan abin ba, bai yarda ya girmama mutanen Kano ba, bai yarda cewa Kannywood ko kuma harkar fina-finai na Hausa cewa hanya ce ta sadarwa wacce zata haskaka addini da al’ada ba, a yanda mutanen Kano suke ko waye shi mun hakura da shi, koda kuwa Kyamara ce ta haife shi”.

“Shi wannan jarumi ya riga yayi bayani shi ba zaibi ka’idoji na mutanen jihar Kano ba, kuma ba zai girmama su ba, to menene zai zo ya nunawa mutanen jihar Kano”.

Afakallah ya kara da cewa dokar hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ita ce duk mutumin da baiyi rijista ba, to babu wani abu da zai taso na Kano yazo yayi, mu kuma mu kyaleshi.

Sai dai Adamu Zango ya karyata labarin cewa ya yanke hurda da jihar Kano, inda ya ce ya yanke hurda ne da masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood ba da al’ummar jihar Kano ba.

Anyi shagalin bikin jaruma Maryam Ceeter

A ranar jumu’ar da ta gabata ne aka daura auren fitacciyar Jarumar fina-finan Hausar nan Maryam Isah Ceeter, a masallacin jumu’a na Alfurkan dake nan Kano.

Jaruma Maryam Ceeter ta wallafa hotunan bikin a shafin ta na Facebook inda masoyanta suka rika yi mata sakon fatan alkhairi.


An sace asusun Jaruma Sadiya Gyale na Instagram

Wasu masu kutse da ba’a san ku su wanene ba sun sace asusun dandalin sada zumunta na Instagram na jarumar fina-finan Hausar nan Sadiya Gyale.

Jaruma Sadiya Gyale ta shaidawa Mujallar Film cewa ta wayi gari masu kutsen sunyi awon gaba da asusun nata na Instagram, inda suke aikawa da wasu sakonni ba tare da sanin ta ba.

A don haka tayi kira ga dukkan masoyan ta, kan su kauracewa dukkan wani sako da suka gani a shafin.

Hoton jaruma Sadiya Gyale

Mahaifiyar Halima Atete ta rasu

A ranar Alhamis din da ta gabata ne Mahaifiyar jaruma Halima Atete ta rasu inda akayi jana’izar ta a birnin Abuja kamar yadda mai shirya fina-finan nan Sheikh Isah Alolo ya wallafa a shafin sa na Instagram.

Hoton jaruma Halima Atete da mahaifiyar ta

Abinda ya sa Deezell ya maka Maryam Booth a Kotu

Mawakin Hip Hop dinnan Ibrahim Ahmad Rufa’I wanda aka fi sani da Deezell ya maka fitacciyar jarumar fina-finan Hausar nan Maryam Booth a gaban kotu.

Cikin wata takardar shigar da kara da mawakin ya wallafa a shafin sa na Twitter ta nuna cewa ya shigar da karar Maryam Booth da wasu mutane biyar a gaban kotu bias zargin yi masa batanci.

Tunda farko dai Jaruma Maryam Booth ta zargi mawakin wanda tsohon saurayin ta ne, da cewa shi ne ya dauki wani bidiyon ta tsirara a lokacin da ta fito daga bandaki, sannan ya fitar da shi aka rika yadawa a kafafan sada zumun ta.

Sai dai mawaki Deezell ya musanta zargin inda ya ce ba shine ya saki wannan bidiyon ba, sannan ya nemi da ta janye zargin da tayi masa ko kuma ya gurfanar da ita a gaban kotu.

Cikin takardar shigar da karar dai ta nuna cewa Ibrahim Ahmad Rufa’I yana neman diyyar zunzurutun kudi har miliyan goma.

Duk da cewa har izuwa wannan lokaci Deezell bai fito ya karyata zargin Maryam na cewa shi ne ya dauki bidiyon ba, sai dai kawai ya musanta sakin bidiyon ga al’umma.

Deezell ya wallafa cewa yanzu haka kotu ta baiwa ‘yan sansa umarnin cigaba da bincike kan al’amarin kafin haduwa a gaban kotu.

 Abba Almustapha ya kammala digirinsa na farko

Fitaccen jarumin fina-finan Hausar nan Abba Almustapha ya karbi sakamakon kamala karatun digirin sa na farko a bangaren kimiyyar dakin karatu.

Abba Almustapha ya wallafa hotonsa da kuma sakamakon karatun nasa a shafin sa na Facebook wanda ya nuna cewa ya kammala karatun da matakin Digiri mataki na biyu a jami’ar Bayero dake nan Kano.

Al’umma da dama sun aike masa da sakon fatan alkhairi akan hakan.

Za’a Karrama Gwamna Bawa Mai Kada

A ranar Lahadin nan ne za’a gabatar da taron bada lambar yabo ga fitattun mutane a jihar Plateau.

Cikin wadanda za’a karrama kuwa akwai fitaccen mai shirya fina-finan nan kuma mai bada umarni sannna Jarumi wato Sani Mu’azu wanda akafi sani da Bawa Mai Kada a shirin wasan kwaikwayon nan na Kwana Casa’in.

Hoton jarumi Sani Mu’azu

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!