Kiwon Lafiya
Shugaba Buhari ya aikewa majalisar dattawa bukatar kara biliyan 164 cikin kasafin bana
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya aikewa majalisar dattawa wasikar bukatar neman sahalewar ta domin kara naira biliyan dari da sittin da hudu wajen cikin kasafin kudi na bana.
Haka kuma cikin wasikar shugaba Buhari ya kuma bayyana cewa gwamnatin tarayya zata yi amfani da wani kaso daga cikin kudaden a babban zaben shekarar 2019 da ke gabatowa.
A cewar wasikar wadda shugaban majalisar dattawa Abubakar Bukola Saraki ya karanta gaban zauren majalisar yayin zaman ta na yau, ta ruwaito cewa shugaba Buhari na cewa za’a yi amfani da naira biliyan dari biyu da arba’in da biyu wajen gudanar da zaben shekarar badi.
A cewar shugaba Buhari naira biliyan dari da sittin da hudu da aka ware domin karawa a kasafin an yi shi ne da nufin bawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC fara gudanar da shirye-shiryen tunkarar zaben.
Cikin wasikar shugaba Buhari ya kuma bukaci majalisun tarayya da su cire naira biliyan dari biyu da ashirin da takwas daga cikin naira biliyan dari biyar da saba’in da takwas da yace sunyi cushe a kasafin shekarar da muke ciki domin gudanar da wasu manyan ayyuka, kamar yadda suka bayyana a baya.