Labarai
Shugaba Buhari ya bada umarnin tsas-tsaura matakan tsaro a jihar Borno
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ba da umarnin daukar tsas-tsauran mataki kan ‘yan ta’adda, sakamakon kisan gillar da ake zargi ‘yan Boko Haram sun yi ga wasu masu gudanar da jana’iza guda sittin a jihar Borno.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu.
Sanarwar ta ruwaito Malam Garba Shehu na cewa, jami’an tsaron kasar nan sun tabbatarwa shugaba Buhari cewa, za su yi duk me yiwuwa don ganin sun ladaftar da wadanda ke da hannu cikin faruwar lamarin.
A cewar Malam Garba Shehu ta cikin sanarwar, shugaba Buhari, ya kuma ce gwamnatin sa za ta ci gaba da aiki tukuru, wajen ganin ta kare rayuka da dukiyoyin al’ummar kasar nan.
Haka zalika shugaba Buhari ya kara da cewa, tuni sojoji su ka bazama farautar ‘yan ta’addar ta sama da kasa domin tabbatar da cewa duk wadanda su ka kai harin ba su tsira ba.