Labarai
Shugaba Buhari ya bukaci kasashen Afrika su yi amfani da lambar katin dan kasa wajen ciyar da harkokin Dimokuradiyya da inganta tsaro
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga kasashen yankin Afrika da su yi amfani da muhimmancin da lambar katin shaidar dan kasa ke da shi wajen ciyar da harkokin Dimokuradiyya da kuma inganta tsaro.
Shugaba Buhari wanda ya samu wakilcin Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha shine ya bayyana hakan a yayin bikin bude taro kan muhimmancin da lambar katin shaidar dan kasa ke da shi karo na 4 da ke gudana a Abuja
Taron da ya hadar da masu ruwa da tsaki a yankin na Afrika zai mayar da hankali kan muhimmancin tattara bayanan kowa ta hanyar yanar gizo ke da shi wanda ya ce hakan zai kara tabbatar da zaman lafiya da kuma inganta dimokuradiyya.
Shugaba Buhari ya kuma jaddada bukatar da ke akwai ga kasashen Afrika da su rungumi ci gaban da duniya ta zo da shi na ta’ammali da yanar gizo wajen tattara bayanan kowa don inganta Dimokuradiyya da inganta tsaro.
Sannan kuma ya ce hakan zai share hanya ga matasan nahiyar Afrika wajen fadada tunanin su don bunkasa harkokin kimiyya da fasaha a yankunan.