Connect with us

Kiwon Lafiya

Shugaba Buhari ya bukaci ’yan Najeriya su zabi duk dan takarar shugaban kasa da ya kwanta musu a rai

Published

on

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bukaci al’ummar kasar nan da su fito gobe Asabar su zabi dan takarar shugaban kasa da ya kwanta musu a rai.

Ya kuma shawarci al’umma da su kada wa dan takarar da suke da kwarin gwiwa kansa zai iya kai kasar nan ga gaci.

Shugaba Buhari ya bayyana hakan ne yayin jawabin da ya gabatarwa al’ummar kasar nan da safiyar yau Juma’a.

Ya ce a matsayinsa na shugaban Najeriya yana kira ga al’umma wadanda ke da katin zabe na din-din-din da su feto gobe Asabar zuwa rumfunan zabe domin zabar shugabannin da suka kwanta musu a rai.

Sai dai shugaban kasar kafin kammala jawabin na sa ya bukaci jama’a da su gudanar da lamuran da suka shafi zaben cikin tsanaki ba tare da hargitsi ba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!