Labarai
Shugaba Buhari ya gana da sufeton yan sanda ta kasa kan arangamar yan Shi’a
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gana da babban sufeton ‘ya sandan kasar Muhammad Adamu kan sabuwar arangamar da jami’an tsaro suka yi da mabiya Shi’a jiya a Abuja, da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane ciki har da mataimakin kwashinan ‘yan sanda.
A zantawarsa da manema labarai bayan kammala ganawar, babban sufeton ‘yan sandan Muhammad Adamu ya ce makasudin ganawar shi ne don shaidawa shugaba Buhari al’amarin da ya faru da kuma hanyoyin bi don magance sake aukuwar hakan a nan gaba.
Cikin wata sanarwa da ta fitar kungiyar Shi’ar ta ce an kashe ma ta mabiya 11, yayin da ita kuma kugiyar nan mai rajin hakkin dan adam Amnesty International ke cewa ta samu rahoton mutuwar mutane 6 nan take yayin hatsaniyar.
Ita kuwa hukumar ba da agajin gaggawa ta kasa NEMA ta bakin babban jami’in yada labaranta Sani Datti, cewa ta yi an kona ma ta manyan motocin daukar marasa lafiya guda biyu.
Sani Datti ya kara da cewa tuni darakta janar na hukumr ta NEMA Injiniya Mustapha Maihaja ya ziyarci inda aka kona motacin don ganewa idonsa abinda ya faru.