Labaran Kano
Shugaba Buhari ya mika alhininsa ga rasuwar tsohon manajan gungun tashar Freedom
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana alhininsa game da rasuwar mataimakin shugaban kungiyar Editoci ta kasa (NGE) Malam Umar Sa’idu Tudunwada
A cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba Shehu; ta ruwaito shugaba Buhari na cewa, mutuwar Umar Sa’idu Tudunwada, babban rashi ne ba wai kawai ga duniyar ‘yan jaridu ko iyalansa da jihar Kano ba, babban rashi ne ga kasa baki daya.
A cewar shugaba Buhari ta cikin sanarwar, Malam Umar Sa’idu Tudunwada mutum ne nagari kuma kwararre wanda ya sadaukar da rayuwar sa wajen gudanar da ayyukan al’umma.
Shugaban kasar ta cikin sanarwar ya kara da cewa, yana alfahari da Malam Umar Sa’idu Tudunwada sakamakon rawar da ya taka wajen fede gaskiya komai dacinta da kuma zage dantse wajen ganin lamura sun kyautatu a kasar nan.
Haka zalika ta cikin sanarwar dai shugaban kasar ya kuma mika da sakon ta’aziyyar sa, ga kungiyar editoci ta kasa (NGE), da gwamnatin jihar Kano da kuma ‘yan uwa da iyalan marigayin, yana mai fatan All.. ya jikan sa, ya gafar ta mai kura-kuran sa.
Rahotanni sun ce Malam Umar Sa’idu Tudunwada, ya rasu ne a jiya a yankin karamar Hukumar Kura sakamakon wani hatsari da ya ritsa da shi da matar sa da ‘yarsa’ wadanda suka fito daga Abuja.