Connect with us

Kiwon Lafiya

Shugaba Buhari ya nuna alhininsa da labarin mutuwar mutane 18 a jihar Lagos

Published

on

Shugaban kasa Muhamamdu Buhari ya ce ya girigiza matuka da jin labarin mutuwar mutane 18 ciki har da dalibai, sanadiyar rushewar ginin mai hawa3 dake yakin Faaji a jihar Lagos.

Muhammadu Buhari ya aike da ta’aziyyar sa ga gwamnatin jihar da iyalan wadanda suka rasa ‘yan uwan su, yayin da fatan wadanda suka sami raunika

Shugaban kasar ya kuma yabawa masu aikin ceto bisa namijin kokarin da suka yi wajen ceto wadanda suka sami raunika.

Muhammadu Buhari ya kuma yi kira ga gwamnatin jihar da ta dauki da ta tabbatar ta dauki matakan da suka dace wajen hana faruwar hakan anan gaba.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Freedom Radio Dutse 99.5 FM Dala FM Kano 88.5

Now Streaming

Archives

Copyright © 2019. Freedom Radio Group. All Rights Reserved.

error: Content is protected !!