Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Kiwon Lafiya

Zabe:Rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi ta kama mutum 52 da zargin tashin-hankali

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kogi ta kama mutum 52 da ta zarge sun haddasa  tashin-hankali a ranar 9 ga watan da muke ciki na Maris wanda aka gudanar da zaben gwamna da ‘yan majalisu a fadin kasar nan.

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Hakeem Busari ne ya bayyana hakan ga manema labarai a birnin Lokoja, yana mai cewa, yawancin wadanda suka kama, sun kama sune a ranar da aka gudanar da zabe gwamnoni da ‘yan makalisu, wanda ake zargin sun sace akwatin zabe tare haddasa tashin hankali.

Hakeem Busari ya kara da cewa, wadanda suka kama sun hada da  Segun Olu da Yakubu Zakari da Salifu Mohammed Ajeshola Michael da Sabiu Halidu da Adamu Idris da Ojoma Eugene da  Sunday Abuda  Isaac Edoh da  Joshua Ejibo da  Ojogo Alhaji da kuma Monday Amodu.

A cewar kwamishinan an kama Segun Olu sakamakon harbin daya daga cikin ma’aikatan hukumar zabe mai zaman Kanta ta kasa INEC da kuma guda daga cikin masu kada kuri’a wanda yayi yunkurin sace akwatin zabe a yankin Egbe da ke karamar hukumar Yagba ta yamma.  

Hakeem Busari ya kuma ce, a wadanda aka kama din 12 daga cikin ‘yan zauna garin banza ne yayin sauran Arba’in din an kama sune bisa zargin su da sace mutane da kuma satar shanu hadi da bangar siyasa.

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!