Labarai
Shugaba Buhari ya taya shugaban kungiyar kwadago murna lashe zabe
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya shugaban gamayyar kungiyar kwadago ta kasa NLC Ayuba Wabba murna, yayin da ya masa fatan ya kammala wa’adin sa cikin nasara, bayan da ya lashe zaben da aka gudanar ba tare hamayya ba.
Har’illa yau shugaban ya taya sauran wakilan gamayyar kungiyar kwadagon Ta NLC a yayin babban taro karo na 12 da kungiyar ta yi a Abuja
Wannan na kunshe cikin sanarwar da fadar shugaban ta fitar cewa shugaban kasar wanda yake neman a sake zaben sa, ya ce zai aiki tare da Ayuba Wabba, da kwamishin zartarwar kungiyar da kwamitin gudanarwar kungiyar ta kasa wanda hakan za sake karfafa dankwan dangantaka da gwamnati da kungiyar ta kwadago.
Daga cikin wadanda aka zaba ba ba tare hamayya ba,da akwai mataimakin shugaban kasa kungiyar na farko Amaechi Asuguni sai na 2 Muhammed Idris da kuma na 3 Najim Yasim.
Sauran su ne ma’ajin kudi Ibrahim Khalil sai mataimakin shugaba kungiyar na farko Abdulrafiu Adeniji sai na 2 Peter Adeyemi da na 3 Lawrence Amaechi da na 4 Oyelekan Lateef da na 5 Mercy Okezie da kuma shugaban kwamitin amintattu na kasa Adewale Adeyanju da dai sauran su.