Kiwon Lafiya
Shugaba Buhari: za’a adaidaita mafi karancin albashi
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce za a iya ragewa wadanda ke daukar albashin sama da naira dubu talatin kudin su na albashi, domin dai-daita al’amarin mafi karancin albashi na naira 30.
Rahotanni na nuni da cewa ba lallai ne sabon Karin mafi karancin albashi ya shafi manyan ma’ikata ba, inda shugaban kasar ya ce ya kamata manyan ma’ikatan kasar nan su fahinci hakan.
Gwamnatin dai za ta fara tattaunawa ne da shugabanin kungiyoyin kwadagon, matukar ta mika kunshin kudirin yarjejeniyar mafi karancin albashin ga majalisun kasar nan domin amincewa.
Shugaban kasar ya yi wadannan kalamai ne ya yi kaddamar da kwamitin bada shawarwari kan yadda za a kaddamar da sabon mafi karancin albashin.
Wannan dai na zuwa ne awanni 24 bayan da gwamnatin tarayya da kungiyar kwadago suka amince za a mika kunshin yarjejeniyar gaban majalisun kasar nan kafin nan da ranar 23 ga watan janairun da muke ciki.