Labarai
Shugaba Buhari zai kai ziyara jihar Nassarawa gobe don kawo karshen rikicin manoma da makiyaya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kai ziyara jihar Nasarawa a gobe Talata a wani bangare na lalubo hanyoyin dakile rikicin manoma da makiyaya dake yawan aukuwa a yankin.
Wasu daga cikin Al’ummar jihar ta Nasarawa na ganin cewa ziyarar ta shugaban kasa zata taka muhimmiyar rawa wajen magance rikice-rikicen Fulani da Makiyaya.
Mataimakin gwamnan jihar ta Nasarawa kan harkokin matasa, dalibai da kungiyoyi masu zaman kansu Mr. Samuel Akala ya bayyana cewa ziyarar ta shugaba Buharin da kuma tattaunawa da masu ruwa da tsaki da shugabannin al’umma babban Al’amari ne da ka iya dawo da zaman lafiyar da aka rasa tsakanin manoma da makiyaya.
Ya kuma kara da cewa ya tabbatar da cewa shugaba Muhammadu Buhari na da masaniya kan hargitsin da ake samu a jihar kuma ya dauki matakan da suka kamata don haka yace ziyarar zata kuma kwantar da hankalin al’ummar jihar.