Labarai
Shugaba Buhari zai kai ziyara kasar Saudiyya
A yau Talata ne ake saran Shugaba kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Saudiyya a wata ziyara ta karshe da zai kai wata kasar waje a matsayin shugaban kasa.
Shugaban zai shafe kusan mako guda, inda ake saran zai dawo gida Najeriya a ranar 19 ga watan Afrilun da muke ciki.
A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban kasa kan kafafen yada labarai malam Garba Shehu ya fitar, ya ce, Shugaba Muhammadu Buhari zai kuma gudanar da aikin Umrah yayin ziyarar tasa.
Sanarwar ta kuma ce Shugaba Buhari zai samu rakiyar manyan mukarraban gwamnatinsa a wannan ziyara zuwa kasar Saudiyya.
You must be logged in to post a comment Login