Labarai
Shugaba Buhari zai tafi Ghana domin halartar taron ƙoli na shugabannin yankin tekun Guinea
Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai tafi kasar Ghana domin halartar taron ƙoli na shugabannin ƙasashen yankin tekun Guinea da za a gudanar a Accra babban birnin ƙasar.
A cikin wani saƙo da fadar shugaban ƙasar ta wallafa a shafinta na Tuwita, ta ce, shugaban zai bar gida Najeriya a yau Talata, inda shugaban ƙasar Ghana Nana Akuffo-Ado zai jagoranci taron.
Ana sa ran shugaban zai gabatar da jawabi a taron wanda zai tattauna dabarun ƙarfafa zaman lafiya da tsaro da yaƙi da masu aikata miyagun laifuka a gaɓar tekun yankunan ƙasashen.
Yayin halartar taron, shugaban zai samu rakiyar ministan harkokin ƙasashen waje Geoffrey Onyeama, da mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Babagana Monguno mai ritaya, da daraktan hukumar tattara bayanan sirri Ambasada Ahmed Rufai Abubakar, da sauran jami’an gwamnati.
You must be logged in to post a comment Login