Labarai
Shugaba Joao Lourenco na Angola ya gabatar da shawarwarin kawo ƙarshen rikicin gabashin Congo DR

Shugaban Angola, Joao Lourenco, ya gabatar da wasu shawarwari domin kawo ƙarshen rikicin da ke faruwa a gabashin Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Congo, kamar yadda fadar shugaban ƙasar Congo ta ruwaito.
An bayyana shawarwarin a matsayin masu matuƙar ban sha’awa, amma ba a fitar da cikakkun bayanai ba.
Ofishin shugaban Angola ya ce ya gana da takwaransa na Congo, Felix Tshisekedi, a Luanda na tsawon sa’o’i domin tattauna rikicin da kuma ƙoƙarin kawo ƙarshen sa.
Tshisekedi ya bayyana cewa shawarwarin Lourenco na iya taimakawa matuƙa wajen neman zaman lafiya.
You must be logged in to post a comment Login