Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labaran Wasanni

A kawo karshen rikicin hukumar AFN – ‘Yan wasa

Published

on

‘Yan wasan guje-guje da tsalle-tsalle a Najeriya sun koka kan rikicin da hukumar take fama dashi tare da yin kira ga mahukunta a hukumar da su kawo karshen rikicin don samun shugabanci na gari.

‘Yan wasan sunyi amfani da kafafen sada zumunta wajen bayyana takaicin su tare da korafi kan rashin samun walwala da jin dadi da sauran su.

An dai samu sabani tsakanin hukumar ta AFN da jami’an dake sanya idanu a harkokin wasanni daga ma’aiakatar wasanni ta kasa a yayin wani taro da aka gudanar a garin Awka dake jihar Anambra a watan Disambar bara.

Hakan ya sanya wani bangare da mataimakin shugaban hukumar Olamide George ke jagoranta yin ikirarin cewa sun dakatar da shugaban hukumar Ibrahim Shehu Gusau.

Lamarin dai ya tilastawa Shehu Gusau fadawa ma’aikatar wasannin cewa AFN hukumace mai cin gashin kanta.

Haka zalika, Gusau ya kuma shigar da kara a gaban babbar kotu dake zamanta a birnin tarayya Abuja yana kalubalantar ma’aikatar wasanni cewa har yanzu shine shugaban hukumar ta AFN a watan Yuli da ya gabata.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!