Ƙetare
Shugaba Macky Sall ya umarci yan sanda su dauki mataki kan zanga-zangar magoya bayan Ousmane Sonko
Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya bai wa ƴan sanda umarnin daukar matakan da suka dace domin ganin an samar da tsaro, bayan mummunar zanga-zanga da magoya bayan madugun ƴan adawa Ousmane Sonko ke ci gaba da yi kan shari’ar da ake yi masa.
Mutum ɗaya ne ya rasa ransa a artabun tsakanin magoya bayan mista Sonko da kuma ƴan sanda.
Rahotonni sun bayyana cewa,an yi ta yin zanga-zanga a birane da ke faɗin ƙasar kan shari’ar da ake yi wa Sonko kan zargin ɓata sunan ministan yawon buɗe idanu wanda mamba ne a jam’iyyar mista Sall.
Sai dai Mista Sonko ya ce, ana yi masa shari’ar ne kawai don hana shi tsayawa takarar kujerar shugaban ƙasa a zaɓen badi.
You must be logged in to post a comment Login