Connect with us

Labarai

Shugaba Tinubu na shirin bai wa yan Nijeriya bashin miliyan 100 don sayen gida

Published

on

Shugaban kasa  Bola Ahmad  Tinubu, ya sanar da shirin bai wa ’yan Nijeriya bashin kuɗin sayen gida har Naira miliyan 100, kan Kudin  ruwa na kaso 9 da digo 75 cikin 100, wanda za’a biya cikin wa’adin shekaru 20.

 

Tinubu ya ce shirin, wanda ake gudanarwa ta Asusun Zuba Jari a Bangaren Gidaje na MOFI (MREIF) mai jarin Naira tiriliyan ɗaya, na daga cikin ƙoƙarin gwamnatin sa na sauƙaƙa wa al’ummar  kasa mallakar gidaje maimakon ci gaba da biyan haya.

 

A cikin saƙon da ya wallafa a shafinsa na X yau  Talata, shugaban ya bayyana cewa masu cin gajiyar shirin za su biya kaso 10 cikin 100 na kuɗin gidan a matsayin kuɗin farko.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!