Labarai
NAPTIP ta samu rahotannin laifukan safarar mutane 1,508 tare da kama mutum 1,434 da ake zargi

Hukumar Hana Safarar Mutane ta Najeriya NAPTIP, ta samu rahotannin laifukan safarar mutane 1,508 tare da kama mutum 1,434 da ake zargi da aikata laifukan tsakanin watan Agustan 2025 zuwa Nuwamban 2026.
Daraktar Janar ta hukumar, Binta Bello ce, ta bayyana hakan yayin wani taro a Abuja.
Ta ce hukumar ta kuma ceto tare da kula da waɗanda aka yi safarar su har mutum 2,700 a tsakanin wannan lokacin.
Ta ƙara da cewa mutane 97 an yanke musu hukuncin, yayin da aka gurfanar da wasu mutane 85 a gaban kotu.
Ta ce tun bayan kafa hukumar, ta ceto tare da tallafa wa mutane 28,762 da aka yi safarar su, sannan ta samu nasarar hukunta mutane 857 bisa laifin safarar mutane
Ta kuma yi kira da a buɗe ofishin NAPTIP a Jihar Delta, wadda ita ce kaɗai jiha da har yanzu ba ta da ofishi.
You must be logged in to post a comment Login