Labarai
Shugaba Tinubu ya magantu kan zabukan cike gurbi a Kano

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya buƙaci masu zaɓe, jami’an tsaro da Hukumar INEC su gudanar da zaɓe cikin tsari da lumana a zaɓen cikin gurbin kujerun majalisun jiha na Ungogo da KMC da ake yi ranar Asabar a Kano.
Wannan na cikin sanarwar da Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin yaɗa labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Jumuʼa 20 Fabrairu 2026 game da zaɓukan da za a gabata a mazaɓun Kano Municipal da Ungogo a Jihar Kano, da jiha Rivers da kuma zaɓen shugabannin ƙananan hukumomin Babban Birnin Tarayya Abuja.
Shugaban ƙasar ya buƙaci duk masu zaɓen da suka cancanta su fito su kaɗa ƙuri’a ba tare da tsoro ba, ya kuma gargaɗi jami’an tsaro da su guji duk wasu tsauraran matakai ko abin da zai iya hana jama’a yin zaɓe.
Ya kuma roƙi jam’iyyun siyasa da magoya bayansu su kauce wa tashin hankali da kalaman da za su iya lalata sahihancin zaɓen.
Sanarwar ta ƙara da cewa, shugaban ya buƙaci INEC ta tabbatar da ingantaccen tsarin tantance masu zaɓe, tafiyar da zaɓe cikin sauƙi da kuma sanar da sakamako cikin lokaci daidai da dokar zaɓe ta 2026.
You must be logged in to post a comment Login