Labarai
Shugaba Tinubu ya sauka a kasar Kenya don halartar taron koli

Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya isa birnin Nairobi na kasar Kenya don halartar taron kolin Afirka da Faransa da aka shirya gudanarwa tsakanin yau da gobe.
Taron mai taken “Afirka ta ci gaba: Haɗin gwiwar Afirka da Faransa don kirkire-kirkire da ci gaba,” zai tattauna kan muhimman batutuwan da suka shafi nahiyar, ciki har da sauyin makamashi, masana’antu masu zaman kansu, ayyukan sauyin yanayi da kuma gyare-gyaren tsarin kuɗaɗen duniya.
Daga cikin waɗanda suka tarbi shugaba Tunibu akwai Ministan Masana’antu da Zuba Jari, Dakta Jumoke Oduwole da Ministan Muhalli Balarabe Abbas Lawal da Ministan Noma da Tsaron Abinci Sanata Abubakar Kyari da Ministan Harkokin Waje Ambasada Bianca Odumegwu-Ojukwu da Ministan Harkokin Waje Ambasada Sola Enikanolaye.
You must be logged in to post a comment Login