Connect with us

Labarai

Farfesa Pantami ya magantu kan zargin da ake masa na mayar da akwatin zaɓensa Abuja

Published

on

Tsohon ministan sadarwa na kasa Farfesa Isa Ali Pantami ya yi ƙarin haske kan zargin da ake masa na dalilin da ya sa ya taɓa mayar da akwatin zaɓensa zuwa Abuja daga Gombe.

 

A hirarsa da gidan talabijin na TVC a yau jiya Lahadi, Pantami wanda ɗaya ne daga cikin masu neman tikitin takarar gwamnan jihar Gombe a zaɓen 2027, ya kuma yi tsokaci kan zargin da ake masa na watsi da lamuran jam’iyyar ta APC na tsawon lokaci.

 

Pantami ya ce ya maida akwatin zaɓensa zuwa Abuja ne a shekarar 2019 saboda muƙamin da ya riƙe na shugaban hukumar NITDA a lokacin, kuma yana daga cikin masu jagorantar abubuwan da suka shafi bayanan intanet da suke da alaƙa da zaɓen, wanda hakan ya sa ake buƙatar kasancewrasa a birnin tarayyar ƙasar.

 

Amma ya ce yanzu haka ya maida akwatin zaɓensa jihar Gombe.

 

A ƴan kwanakin nan dai Pantami ya ɗauki hankalin ƴan Najeriya, tun bayan da jam’iyyarsa ta APC ta amince da miƙa tikitin takarar gwamnan jihar Gombe ga Jamilu Isiyaku Gwamna bisa tsarin masalaha, abin da Farfesan ya yi watsi da shi, inda ya ce zai yaƙi “rashin adalcin da aka yi”.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!