Freedom Radio Nigeria

Freedom Radio Nigeria

Labarai

Shugaba Tinubu ya umarci jami’an tsaro su kuɓutar da ɗaliban Zamfara

Published

on

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya umarci jami’an tsaro kan su kuɓutar da sauran ɗalibai mata na Jami’an Tarayya da ke Gusau a jihar Zamfara, da masu garkuwa da mutane suka sace.

Cikin sanarwar da mai magana da yawun shugaban, Ajuri Ngelale ya fitar, Tinubu ya yi Allah wadai da sace ɗaliban da aka yi ranar Juma’a.

Haka kuma yana mai cewa wannan abu ne na rashin tausayi da imani kan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.

Shugaba Tnubu ya kuma tabbatar da cewa a shirye gwamnatinsa ta ke wajen kare dukkan al’ummar Nijeriya.

Haka kuma shugaban, ya sha alwashin yi duk mai yiwuwa domin kuɓutar da ɗaliban.

Click to comment

You must be logged in to post a comment Login

Leave a ReplyCancel reply

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 Your browser does not support the audio element. https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!