Labarai
Shugaban APC ya kai wa Sanata Hanga ziyara

Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya kai wa Sanata Rufa’i Sani Hanga ziyara a gidansa da ke Abuja a daren jiya Laraba.
Mai taimaka wa Sanatan kan harkokin yaɗa labarai, Umar Saminu Mai-Adashi, ya ce ganawar ta gudana cikin yanayi na fahimtar juna inda suka tattauna kan batutuwan siyasa da ci gaban ƙasa.
Ya ce tattaunawar ta mayar da hankali ne kan yadda za a ƙarfafa dimokuraɗiyya da kuma bunƙasa ci gaban Najeriya,sai dai wannan ziyara ta ƙara haifar da hasashen cewa Sanata Hanga na iya sauya sheƙa daga jam’iyyarsa, musamman bayan ya nuna rashin jin daɗinsa kan yadda ake mu’amala da shi a cikin jam’iyyar NDC.
A baya-bayan nan Sanata Hanga ya bayyana cewa an cire shi daga jerin waɗanda aka amince da su a matsayin ‘yan takarar sulhu na jam’iyyar, lamarin da ya hana shi damar sake neman kujerar Sanatan Kano ta Tsakiya.
You must be logged in to post a comment Login