Ƙetare
Shugaba Trump ya sauka a birnin Tokyo na Japan

Shugaba Trump na Amurka ya sauka a birnin Tokyo na ƙasar Japan a wata ziyara da ya ke yi a yankin Asia.
Mista Trump zai gana da Sarki Naruhito kafin ganawarsa da sabuwar firaiministar ƙasar, Sanae Takaichi.
Ms Sanae Takaichi ta ce, ƙarfafa ƙawancen tsaro tsakanin Amurka da Japan ne babban abin da ganawar tasu za ta mayar da hankali.
Kasar Japan dai ta zuba biliyoyin daloli cikin tattalin arzikin Amurka, lamarin da ya sa wasu ke ganin dalilin da ya sa ta tsallake harajin da Trump ya ƙaƙaba wa wasu ƙasashe kenan.
You must be logged in to post a comment Login