Addini
shugaban Cocin Anglican ya soki kasashe masu arziki da suka daina tallafawa kasashe matalauta.
Shugaban cocin Ingila Rabaran Justin Welby ya soki kasashe masu arziki sakamakon suke aljihunsu da su ka yi wajen taimakawa kasashe matalauta.
A cewar sa ba daidai bane kasar Burtaniya ta suke aljihunta ga kasashe ‘yan rabbana ka wadata mu.
‘‘Cutar covid-19 ta koya mana abubuwa masu yawa, mafi muhimmanci ciki kuwa shine dukkannin mu mun dogara da juna don samun tsira daga cutar ta corona’’
‘‘Saboda haka ‘yancin mu, kariyar mu, lafiyar mu da na iyalan mu har ma da addinin mu: Duk suna da matukar muhimmanci gare mu’’
‘‘A don haka babu dalilin da lokacin taimako zai zo sai kuma mu suke bakin aljihunmu wajen taimakawa wadanda ke bukatar taimako’’ a cewar Justin Welby.
Shugaban cocin na Anglican ya kuma ce kamar yadda burtaniya ta shige gaba wajen samar da allurar riga-kafin cutar corona to wajibi ne gareta ta kara kaimi wajen yaki da sauyin yanayi.
Rabaran Justin Welby ya kuma ce duniya ta ga yadda kasashe irinsu: Yemen, Syria da Sudan ta kudu suka shiga biyo bayan yanke musu tallafi da kasashe masu karfin arziki su ka yi, saboda haka ya bukaci duniya da ta dunkule wajen taimakawa juna.
You must be logged in to post a comment Login