Kiwon Lafiya
Shugaban kasa Muhammadu Bahari ya shirya buda baki a Saudiyya
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gudanar da taron buda baki a jiya lahadi a birnin Makka tare da gwamnan jihar Zamfara Abdul’aziz Yari da kuma Sarkin Maradun Garba Tambari.
Babban Mataimakin shugaban kasa kan harkokin yada labarai Malam Garba shehu ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar jiya Lahadi a babban birnin tarayya Abuja.
Ya ce a yayin buda bakin shugaba Buhari ya bayyana takaicin sa kan yadda ake samun kashe-kashen mutanen da basu ji ba basu gani ba da kuma bannatar da dukiya a jihar Zamfara.
Mataimakin shugaban kasar ta cikin sanarwar ya kuma bayyana cewa shugaba Buhari ya yi alkwarin yin duk mai yiyuwa wajen maganin ayyukan ta’addanci da kuma kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Da ya ke gabatar da addu’a a yayin taron, Sarkin Maradun Alhaji Garba Tambari ya yi addu’ar All.. ya jikan wadanda suka mutu sakamakon ayyukan ta’addanci da kuma fatan samun dawamammen zaman lafiya a Najeriya baki daya.
Sanarwar ta kuma ruwaito cewa cikin wadanda suka halarci taron sun hadar da jakadan Najeriya a Kasar Saudi Arabiya Justice Isa Dodo da sauran mataimaka na musamman ga shugaban kasa.