Labarai
Shugaban kasa ya taya wazirin Dutse murnar cika shekaru 70
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Wazirin Dutse Alhaji Bashir Dalhatu murna wanda ya cika shekara saba’in da haihuwa a jijya Alhamis.
Muhammadu Buhari y ace taya murna ga Bashir Dalhatu ya zama wajibi kasancewar Allah ya albarkaci rayuwar sa cikin wannan shekaru masu yawa da yayi a duniya,.yana aikin gwamnati da kuma bangarori masu zaman kan su.
Sakon taya murnar na kunshe cikin sanarwar da babban mai taimakawa shugaban kasa kan kafafan yada labarai Malam Garba Shehu ya fitar a Abuja a jiya Alhamis.
Haka zalika shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya alummar masarautar Dutse da ‘yan uwa da iyalai da abokan Wazirin Dutse Alhaji Bashir Dalhatu wanda ya taba rike mukamin ministan kula da al’amuran cikin gida da kuma ministan wuta da mumula karafa kuma ya taba zama babban sakatare a ma’aikatar sufuri da jiragen sama.
Gwamnatin Jigawa ta rage wa ma’aikata lokacin aiki
Jigawa:Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 7 a wani batsari da ya afku
Fadar shugaban kasa ta aike da ta’aziyar ta ga Iyalan Tafawa Balewa
A cewar sanarwar shekarun Alhaji Bashir Dalhatu da yayi wajen bautawa kasar sa a matsayin sa na kwararren lauya ba zata taba mancewa da sub a, kuma ba za’a taba Ambato tarihin kasar nan ba tare da sanya irin gudunmawar da ya bayar ba.
A don haka sanarwar ta kara da cewar shugaban kasa ya bukaci da ya cigaba da hidimtawa kasar nan ba tare da gajiyawa ba.