Connect with us

Labarai

Jigawa:Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 7 a wani batsari da ya afku

Published

on

Rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa ta tabbatar mutuwar mutane 7 tare da jikkatar mutane 9, a sakamakon taho-mu-gama da wasu motoci biyu suka yi a karamar hukumar Maigatari da ke Jihar ta Jigawa.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan Jihar Jigawa SP Abdu Jinjiri ne ya tabbatar da hakan yana mai cewar an mika gawarwakin wadanda suka mutu zuwa babban Asibitin garin Gumel.

Rahotanni sun bayyana cewa wata mota kirar Fijo 206 mai lambar Tarauni wadda aka ce ta fito daga nan Kano da nufin zuwa Malam Madori, ta kwacewa direban sannan ta karawa wata Golf mai lambar Abuja da ta fito daga Jihar Yobe, a kauyen Kwalande a ranar asabar din da ta gabata.

An dai garzaya da wadanda suka jikkata babban asibitin Gumel don ba su kulawar gaggawa.

 

Listen Live

Freedom Radio Kano 99.5 FM https://stream.zeno.fm/t8bhnmek8mzuv Freedom Radio Kaduna 92.9 FM https://stream.zeno.fm/5z9v4k7e9mzuv Freedom Radio Dutse 99.5 FM https://stream.zeno.fm/wp75as7e9mzuv Dala FM Kano 88.5 https://stream.zeno.fm/9zdvuszaanzuv
error: Content is protected !!